Manyan Labaran Fasaha Na Shekara ta 2015

A journalist tries to use the new device using 3D-heptics technology which gives users tectale and kinethetic feeling virtually at a press preview in Tsukuba, suburban Tokyo on September 1, 2014. Japan's high-tech venture Miraisens unveiled a 3D technolog

Manyam kamfanonin fasahar nan uku da suka hada da Apple da Facebook da Google, sune manyan labaran shekarar 2015.

kandan daga cikin labaran da suka mamaye kanun labarai sune, za’a ga sabuwar motar nan maras matuki da damuwa kan ake satar bayanan mutane kan yanar gizo, sai kuma sababbin kayayyakin da aka fitar wanda suka hada da agogon fasaha na Apple da wayar iPhone 6S da ma kananan jiragen nan marasa matuki , har ma da sabuwar na’urar ‘daukan hoton nan da take ‘daukar dukkan kusurwoyi hudu a lokaci guda.

Kadan daga cikin labaran fasaha da muka kawo muku sune:

Kamfanin Google ya amince daya gayawa mutane masu amfani da shafin sa yadda yake amfani da bayanansu dayake adanawa a lokacin da suke bincike akan shafin, yin hakan ya biyo bayan wani bincike da hukumar kiyaye bayanan mutane a yanar gizo ta Birtaniya tayi, inda ta gano cewar manufofin kamfanin kan kare sirrin bayanan mutane kadaran kadahan ne.

Kantin sayar da kayayyaki mafi girma a duniya, Wal-Mart, ya nemi izni daga hukumomi na Amurka domin yayi gwajin amfani da jiragen sama marasa matuka wajen kai ma jama’a kayan da suka saya gidajensu, da daukar kaya daga gefen kanti da kuma lissafin kayayyakin dake ajiye a dakunan ajiye kayayyakinsa.

Wasu masu bincike a China sun bayyana Mota mai anfani da tunanin dan Adam wajen tuka kanta ba tare da an saka mata hannu ko kafa ba, wadda itace ta farko a China.

Wani jirgin sama da kasar Switzerland ta kera mai amfani da hasken rana, ya sauka a jihar Hawaii, bayan da ya kammala wata doguwar tafiyar zagaya duniya da ba a taba yin irinta ba. Tafiyar da yayi ta kan Tekun Pacific itace mafi hatsari.

Kamfanin Yudala dake sayar da kayyakin sadarwa na zamani ta kan yanar gizo a Najeriya, ya fitar da sanarwar zai fara amfani da jirage maras matuki da ake kira drones a turance don su gaggauta isar da hajoji ga abokan cikini.