Manyan kasashen duniya sun bukaci tsagaia wuta a Siriya - John Kerry

John Kerry da wasu manyan kasashen duniya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada yau Jumma’a cewa, manyan kasashen duniya sun amince zasu bukaci a tsagaita wuta a yakin da ake yi a Syria, kuma ana sa ran matakin ya fara aiki nan da mako daya.

Jan Egeland, shugaban kwamitin Majalisar Dinkin Duniya a taron da ake yi kan batutuwan jinkai a Jamus, inda aka cimma wannan yarjejeniyar, yace “sai tayiwu wannan ne budin da ake dako.”

Miniustan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fada ta shafinsa a dandalin Twitter yau Jumma’a cewa, “wannan mataki yana da muhimmanci kan hanyar samo damar warware rikicin da ake yi a Syria.”

Sai dai anji Firayim Ministan Syria Dmitri Medvedev, yana gargadin manyan kasashen duniya cewa suyi tunani gameda tura sojojin-kasa zuwa Syria. A cikin sanarwa da ya bayar yau Jumma’a, yace, matakin sojin kasa zai iya tsunduma dukkan kasashe dake aiki kan rikicin cikin yaki.

Kerry ya gayawa manema labarai a birnin Munch cewa, shirin tsagaita wutar ba zai shafi kungiyoyin ‘yan ta’adda ba, da suka hada da ISIS, Al-Nusra d a dai sauransu.