Jami’an sun yi murabus din ne bisa dalilin cewa suna so su ba da dama a yi sauye-sauyen da ake yi a hukumar domin a inganta aikinta.
Biyar daga cikin jam’ian, mataimakan shugaban hukumar kwaston din, sun ajiye aikin ne a kan gashin kansu yayin da sauran kuwa ka’ida ce ta hau kan su, wadda ta tanadi cewa duk wanda ya rage kasa da shekara daya ya ajiye aikinsa.
“Jami’an da abin ya shafa, yawansu 34, cikin 34 nan muna da mataimakan shugaban kwastom guda biyar, su suka rubuto da kansu akan niyyarsu ta cewa za su yi ritaya.” In ji Kakakin hukumar Joseph Attah.
Wannan lamari da ya auku a jiya, ya janyo cecekuce a duk fadin kasar, kuma kusan za a iya cewa ba kasafai aka saba ganin haka ya auku a hukumar ba.
A tattaunawar wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa da Mr Attah, ya kuma tambayeshi shin ko wasu ba za su ce dokar da ta shimfida cewa dole sai mutum ya ajiye aikinsa idan ya rage mai kasa da shekara guda ya ajiye aikinsa ta zama tamkar an tilsatawa mutum ya yi ritaya ba ne?
Ku saurari amsar da Mr Attah zai ce a cikin wannan rahoto na Umar Faruk Musa:
Your browser doesn’t support HTML5