Manya Da Kananan Fasahohi Sun Soma Taimakawa Habbakar Kasuwanci Ta Yanar Gizo A Najeriya

Shugaban Najeriya

Fasahohi sun soma yin tasiri a harkokin kasuwanci ta hayar yanar gozo a Najeriya duk da matsalolin kasar.
An saba yin korafi a Najeriya cewa babu abun da yake aiki yadda ya kamata. Hanyar sadarwa da na yanar gizo ba kasafai suke aiki ba. Wani lokacin ma makanikin da zai gyara mota sai a nemeshi a rasa. A irin wannana halin rudani ta yaya wani kamfani mai suna Jumia ya kirkiro da kasuwanci ta hanyar yanar gizo kamar tadda kamfanin Amazon ya keyi a Amurka inda yake shigo da kaya kama daga jambaki zuwa naurar kwafan takardu ya kuma raba a duk fadin kasar Najeriya?

Birnin Legas cibiyar kasuwanci ne a kasar kuma ya yi kamarin suna a kan abubuwa da yawa har da cinkoson motoci da aikata cuta da damfara ta hanyar yanar gizo.
Amma yayin da wasu matasa suka yi tunanin kafa kamfanin kasuwanci ta yanar gizo a farkon shekarar 2012 suna zaton zasu yi anfani da matsalolin su ci riba. Suna tunanin masu saye da sayarwa na yau da kullum zasu guje ma cinkoson hanyar sadarwa su sayi kayan da zasu sayar ta hanyar yanar gizo. Babban daraktan Jumia Tunde Kehinde yace lokacin da suka fara Jumia babu wanda ya yadda yin hakan ya dace sabili da halayan ‘yan Najeriya.

Daukan ma’aikata ya kasance masu da wuya. Haka ma kwastamomin da zasu sayar masu da kaya da wadanda zasu saya suna shakku game da kasuwanci ta yanar gizo a irin kasa kamar Najeriya inji Kehinde.

Da farko sun kwashe wajen makwanni hudu kafin su samu kan yanar gizon su kuma soma aikawa mutane kayan da suka saya. Da ma suka fara sun sha wuya wurin karfafa mutane su amince su shigar da lambar katin kudinsu cikin yanar gizo kamar yadda Raphael Afaedor, daya daga cikin wadanda suka kafa kamfani ya fada.
“Yace ba zamu tsaya har sai mutane sun amince da mu ba. Sai muka soma da kai masu kayan da suka saya idan sun ga kayan kana su biya mu” in ji Afaedor.
Yace sun soma da yin anfani da babura biyar da burin kamfanin ya zama mafi girma a kasuwanci ta yanar gizo a kasar da ma Afirka gaba daya inda mutane fiye da miliyan 160 zasu yi kasuwanci.

Har yanzu suna da jan aiki gabansu amma suna da motoci 160 da ma’aikata 600 suna kuma kai dubban kaya kowace rana.
Kamar kamfanin Amazon Jumia na sayar da kaya iri-iri. To sai dai ba kamar Amazon ba masu kasuwanci a Najeriya dole su daure da gurbatatun hanyoyi da rashin wutar lantarkida da cin hanci da rashawa wadanda suka sa yin kasuwanci a kasar matukar wuya.

Kehinde yace kamfanin ya samu habbaka da sauri domin ya yi la’akari da duk matsalolin da zasu fuskanta. Misali sukan yi anfani da kai kaya kan babura a wuraren da motota bata iya zuwa sabili da rashin hanya. Akwai anfanin yin kasuwanci a Afirka amma dole a yi la’akari da yanayin kasa kada a dauko wani yanayi daban a zo a ce za’a yi anfani da shi.

Kasuwancin yanar gizo abu ne sabo a nan amma Jumia na gasa da wasu kamfanoni biyu Konga.com da DealDey.com.

Wadanda suka saka jari a Jumia sun bude shagunan kasuwanci ta yanar gizo a kasashen Misra da Morocco da Afirka Ta Kudu da Kenya.

Masu hannu da shuni sun saba sayan kaya a shagunan London. Suna fatan yanzu ‘yan Najeriya masu matsakaicin arziki zasu soma sayen kayansu a Najeriya.