Shekaran jiya Laraba likitocin suka shiga yajin aiki na kwanaki biyar da suka kira na gargadi ga gwamnatin kasar. A mayan asibitocin jihar Neja alamura basa tafiya kamar yadda ya kamata. Wasu majinyata ma sun fara kauracewa zuwa asibitocin kudi domin ceton rai.
A asibitin kwararru na IBB dake cikin garin Minna majinyata a asibitin sun ce babu wani likita da ya zo dubasu tun da aka fara yajin aikin. Wasu da suka yi binciken jiki da likitoci suka basu sun kawo sakamakon yau to amma babu likitan da zai duba sakamakon. Haka aka bar su kara zube.
Duk kokarin a ji ta bakin likitocin ya cutura. To sai dai tun makon da ya wuje kungiyar likitocin ta fitar da wata sanarwa da shugabanta na kasa ya sawa hannu Dr Osahon Onabulele cewa zasu fara yajin aiki na gargadi wannan makon. Wannan yajin aikin zai kare ranar Litinin mai zuwa domin a cewarsu gwamnatin Najeriya ta gaza wajen cika masu alkawura na yin gyara a asibitocin kasar da kuma biyansu wasu alawus. Sanarwar ta ce bayan wannan yajin aiki na gargadi idan har ba'a biya masu bukata ba zasu fara yajin aikin na har sai abun da hali ya yi.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.