Mai neman jam’iyar Democrat ta tsaida shi takarar shugabancin Amurka Bernie Sanders ya shaidawa shirin tashar MSNBC Mornin Joe yau juma’a cewa, zai kadawa Hillary Clinton kuri’a a zaben kasa da za a gudanar a watan Nuwamba.
WASHINGTON, DC —
Bernie Sanders yace, hana Donald Trump shiga fadar White House yana daya daga cikin manufofinsa.
ya kara da cewa “ a yanzu haka batun shine, zan yi iyakar kokarina in kada Donald Trum. Ina ji Donald Trump zai zama bala’I ta kowacce fuska idan aka zabe shi shugaban kasa.”
Sanders yaci gaba da yakin neman zabe da kuma jawabi a taruka a fadin kasar, duk da yake Clinton ta sami wakilan da take bukata a farkon watan Yuni, na zama ‘yar takarar jam’iyar Democrat. Ya yi watsi da kiran da ake yi mashi ya janye kafin babban taron jam’iyar na kasa.
Yace, “menene zai hana in yi abinda muka iya yi, yayinda nake kokarin yakin ganin mun sami damar da zamu iya samu. Sandar yace yana nacewa ne da nufin ganin an dama da Amurkawa a tsarin siyasa.