Manuel Pellegrini Ya Koma Spain A Zaman Kocin Betis

  • Murtala Sanyinna

Manuel Pellegrini

Kungiyar kwallon kafar Real Betis ta kasar Spain ta tabbatar da Manuel Pellegrini a zaman sabon mai horar da ‘yan wasan kungiyar, farawa daga kakar wasanni mai zuwa.

Kocin mai shekaru 66 zai karbi aikin ne daga Rubi, wanda kungiyar ta sallama a watan Yunin da ya shige, sakamakon koma baya da kungiyar ta fuskantar.

Yanzu haka tsohon dan wasan kungiyar Alexis Trujillo ne ke shugabancin kungiyar na rikon kwarya bayan korar Rubi.

Pellegrini dan kasar Chile ya rattaba hannu a kwantaragin shekaru 3, da za ta karkare a shekarar 2023.

Tsohon kocin na Manchester City da West Ham United, ya taba fafata gasar La Liga, sa’adda ya yi horar da ‘yan wasan Villarreal, Real Madrid da Malaga a can baya.

Pellegrini yana zaune ne ba aiki tun sa’adda ya raba gari da kungiyar Wast Ham a watan Disamban da ya wuce, bayan watanni 18 yana jagorantar kungiyar.

Ya taba lashe gasar Premier da kuma gasannin League Cup biyu da kungiyar Manchester City tsakanin shekarun 2013 da 2016.