Kamfanonin shafukan sada zumunci da kokarin magance matsalar yada labaran kanzon kurege da akanyi ta kafofin, hakan yasa kamfanin Whatsapp daukar wasu kwararan matakai. Daga ranar Talata mai zuwa kamfanin zai kaddamar da wani sabon tsari wanda zai inganta manhajar tashi.
Kamfanin zai inganta manhajar ne da wani tsari da zai bayyana ainihin tushen labari, ta haka mutum zai iya gane wanda ya kirkiri labari da kuma hanyar da labarin yabi kafin ya iso wayar mutum, hakan zai tabbatar ma mutum sahihancin labarin.
Kamfanin ya sanar da hakan ne a shafin shi na bayanai, wanda yake da yakinin cewar hakan zai ceto rayukan jama’a da dama, wajen ganin an dakile yada labarai marasa tushe. Mutane masu amfani ds tsohuwar manhajar zasu samu tsarin a wayoyin su.
Ta hakan mutum zai iya tabbatar da cewa sakon ya fito daga wani wanda ya sani kamar aboki, dan’uwa, mutane zasu iya sanin labarin da ya kamata su dinga aikawa ko kuma barin shi daga inda suka ganishi don basu da masaniyar tushen sa.