A karon farko da aka aika na’urar robot duniyar wata, don taimakama ma’aikatan sama jannati debe kewa, wadda zata taimakama ma’aikatan gudanar da aikin su yadda ya kamata a duniyar ta wata.
Na’urar da aka yi ma suna Cimon, mai nauyin kilogram 5, zata iya yawo cikin iska a sararrin samaniya. Wannan tsarin na gwaji zai taimaka wajen ganin yadda ma’aikatan sama jannati zasu gudanar da aikin su tare da taimakon na’urar.
Na’urar dai na dauke da kyamara da makirfo wato na’urar kara sauti, wadda zata iya daukar sautin mutun da gane kowa take aiki da shi a cikin jerin ma’aikatan sama jannatin. A kuma duk lokacin da ba’a bukatar na’urar tayi magana za’a iya sata bacci.
Kunbon “SpaceX 9”da aka aika daga sansannin ‘yan sama jannati dake jihar Florida da misallin 05:42 na safe.
Facebook Forum