Manema Daliban Chibok Sun Gana Da Buhari

Nigeria Kidnapped Girls

Larabannan ne masu fafutukar gani an ceto daliban Chibok suka kai ziyara fadar shugaban Najeriya inda suka gana Shugaba Muhammadu Buhari.

Wakilin Muryar AMurka Hassan Maina Kaina ya tattauna da daya daga cikin shuwagabannin gwagwarmayar Hadiza Bala Usman. To ke me suka gaya wa shugaban kasa?

Hadiza tace “mun kai koken mu na maganar ceto ‘yan matan Chibok, mun je fadar shugaban kasa tare da iyayen ‘ya’yan nan da suke hannun Boko Haram, mun je mun tarar da shugaban kasa da mataimakinshi, yayi mana bayani cewa wannan gwamnati ta tashi haikan akan ceto ‘yan matan nan. Gwamnatin shi maganar harkar tsaro shine kan gaba, saboda ya bayyana mana yaje Nijar, yaje Cadi cikin maganganun da yayi da shugaban kasar su akan maganar ceto ‘yan matan nan da fada da yaki da ‘yan Boko Haram.”

Kasan cewar tun ba yau wannan kungiya take wannan gwagwarmaya, kungiyar ta bayyana ra’ayinta game da matakan da aka dauka na ceto wadannan dalibai.

“(Buhari) ya bamu alkawari cewa duk abunda gwamnatinshi zata yi, zata dage haikan ta ceto ‘yan matan nan. Mu dai baza mu bar abunda muke yi ba, zamu cigaba da gangaminmu har Allah Ya sa gwamnatin Najeriya ta ceto ‘yan matan nan,” a cewar Hadiza Bala.

Hadiza ta kara da cewa “mun bayyana mishi (Buhari) cewa gwamnatin Najeriya da lokacin da Goodluck Jonathan yake shugaban kasa, sun ce zasu ceto wadannan ‘yan mata, har sun san inda ‘yan matan nan suke, amma yau kwana dari hudu da hamsin, ba’a ceto su ba.”

Your browser doesn’t support HTML5

Manema Daliban Cibok Sun Gana Da Buhari – 2’30”