Manchester United Ta Kuduri Aniyar Goyan Bayan Sayen 'Yan Wasa.

Ole Gunnar Solskjaer

Ed Woodward, Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yace za su baiwa kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer isassun kudade da kuma duk wani goyon baya da yake bukata wajen sayen ‘yan wasa, domin farfado da martabar kungiyar da ta rasa a idon duniya a kakar wasan da ta gabata in da ta gaza yin nasara.

Kungiyar ta Manchester United ta kammala gasar firimiyar Ingila a bana a mataki na 6 a teburin da maki 66, tazarar maki 32 tsakanin ta da abokiyar karawar ta Manchester City, wadda ta lashe kofin na bana da maki 98 kuma shekaru biyu kenan tana daukar kofin a jere.

Kocin kungiyar Ole Gunnar Solkjaer, ya fara da kafar dama, bayan karbar ragamar horar da United daga hannun Jose Mourinho wanda aka sallameshi, tunda kungiyar ta sami nasara a wasanni 14 daga cikin 17 na farko da ta fafata a karkashin Ole Gunnar.

Sai dai kuma daga bisani a karshen kakar wasan bana, kungiyar ta gaza ci gaba da samun nasara inda wasanni 2 kacal ta iya lashewa daga cikin goma sha biyu da ta fafata.

Hakan ya sa ba zata fafata a gasar cin kofin zakarun Turai na Uefa Champions League na shekara 2019/2020 ba, sai dai ta sami kanta a kungiyoyin da zasu fafata a gasar Europa Cup, wannan wani babban kalubale ne ga 'yan kungiyar.