Manchester United ta bi West Ham har gida ta doke ta da ci 2-1 a gasar Premier League ta Ingila.
West Ham ce ta fara zura kwallo a ragar United a minti na 30 ta hannun Said Benrahman.
Minti Biyar bayan haka, Cristiano Ronaldo ya farke kwallon. Wannan ce kwallonsa ta hudu cikin wasanni uku da ya buga Manchester United tun bayan komen da ya yi.
An tafi hutun rabin lokaci har aka doshi lokacin tashi kafin nan Jesse Lingard ya zura kwallo ta biyu a ragar West Ham.
Hakan ya ba Lingard damar wanke kansa, saboda sanadi da ya yi Young Boys suka ci United a gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA bayan wani kuskure da ya yi.
Sai dai wani abu da ya ja jan hankali a wasan shi ne yadda West Ham ta barar da fenarti ta hannun Mark Noble wanda ya shigo gab da za a kammala wasan.
Har yanzu ba a ci Manchester United a gasar ta Premier ba cikin wasannin da ta buga, inda ta lashe hudu ta yi kunnen doki a daya.
Ita kuwa West Ham, wannan shi ne karo na farko da ta rasa wasanta.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?
Your browser doesn’t support HTML5