Manchester United Ta Dare Saman Teburin Gasar Premier

Paul Pogba

Manchester United ta zauna daram a saman teburin gasar Premier League ta Ingila bayan da ta doke Burnley da ci 1- 0.

Wannan dama ta hawa teburin gasar ita ce ta farko da kungiyar ta samu tun bayan kakar wasa ta 2012-13 a lokacin kungiyar na karkashin kulawar Sir Alex Ferguson.

Kwallon da Paul Pogba ya zira ce ta kai Man U ga wannan nasara bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Hakan kuma ya ba kungiyar damar samun maki ukun da ya sa kungiyar ta yi wa sauran kungiyoyin zarra a teburin gasar.

An dai kwashe zangon farko na wasan ba tare da an zira wata kwallo ba amma da aka dawo daga hutun rabin lokaci a daidai minti na 71, Pogba, ya zira kwallo a ragar Burnley.

Manchester na da maki 36, sai Liverpool da ke biye da ita da maki 33 sai kuma Leicester mai maki 32 a teburin.

A ranar 17 ga watan Janairu Liverpool za ta kara da Manchester United a wasan da ake ganin zai yi zafi.

Leicester za ta kara da Southampton, sai kuma Sheffiled United ta karbi bakunci Tottenham.