Cristiano Ronaldo ya fara da kafar dama a komen da ya yi zuwa Manchster United inda ya zura kwallaye biyu a ragar Newcastle a gasar Premier ta Ingila.
Wannan ne wasan Ronaldo na farko bayan da ya baro Juventus a gasar Italiya ta Seria A a kwanan nan.
Manchester United ta lallasa Newscastle da ci 4-1 a wasan wanda aka buga a Old Trafford.
Ronaldo ya ci kwallon farko ne a karin lokacin da aka yi gab da za tafi hutun rabin lokaci, bayan da aka kwashe minti 45 babu kwallo ko daya daga bangarorin biyu.
Sai dai dan wasan Newcastle Javier Manquillo ya farke kwallon yaran Ole Gunner Solksjaer a minti na 56.
Jim kadan bayan hakan, Ronaldo ya sake zura wata kwallo a ragar Newcastle a minti na 62 abin da ya kai wasan 2-1.
Bruno Fernandes ya ci wata kwallon a minti na 80 sannan Jesse Lingard ya kara wata kwallon a minti na 90.
Ronaldo ya taba buga wa Man U wasa daga 2003 zuwa 2009 kafin daga nan ya koma Real Madrid ya kuma dangana da Juventus.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?
Your browser doesn’t support HTML5