Kungiyoyin kwallon kafar Manchester United da Chelsea sun sami gurbi a gasar zakarun Turai ta kakar wasanni mai zuwa, bayan da duka kungiyoyin biyu suka yi nasara a wasanninsu na karshe na gasar Premier a ranar Lahadi.
Tun a makon jiya ne Liverpool ta daga kofin na gasar Premier ta bana da aka soma tun a ranar 19 ga watan Agustan bara, to sai dai kuma aka dan dakatar da ita na tsawon watanni 3 sakamakon annobar coronavirus.
United ta karkare a matsayin ta 3 teburin gasar ta Premier bayan da ta yi nasarar doke abokiyar takararta Leicester City da ci 2-0, a yayin da ita ko Chelsea ta karkare a matsayin ta 4, bayan da ita ma ta doke Wolves da ci 2-1.
Leicester da ta karkare a matsayin ta 5 tebur ko za ta fafata gasar Europa League a kakar wasanni mai zuwa, tare da Tottenham, wadda ta karkare a zaman ta 6, bayan da ta yi kunnen doki da Crystal Palace da ci 1-1.
A can kasan tebur kuma Bournmouth da Watford sun fadi daga gasar ta Premier kasancewar su a matsayin na 28 da 29 a kasan tebur, inda suka bi sahun Norwich wadda ta sami tabbacin faduwa daga gasar tun a makon da ya gabata.