Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta Ingila, ta yi tattaki har zuwa Paris ta doke Paris Saint Germain mai masaukin baki a wasan semi-final na gasar cin kofin zakarun turai ta UEFA.
An tashi a wasan ne da ci 2-1
Da farkon tashin wasan, PSG ce ta fara farka ragar City inda dan wasa Marquinhos ya zira kwallon farko a minti na 15 da ka.
Kusan daukacin zangon wasan na farko - wato kafin a je hutun rabin lokaci, PSG ce ta yi ta wasan kura da City.
Masu sharhi da dama sun ce, da PSG ta koma bayan hutun rabin lokaci da irin wannan kuzari, da ta kare mutuncinta a gida.
Amma hakan bai samu, domin City shigo-shigo ba zurfi ta yi wa PSG, inda a karshen wasan kocinta Pep Guardiola yake cewa,, ‘yan wansa sun nuna kamar suna jin “kunya” a wasan
A minti na 63 sai ga City ta farke kwallon daga hannun De Bryune, sannan minti takwas bayan haka, sai ga Riyad Mahrez da na shi guzurin a ragar ‘yan wasan Mauricio Pochettino.
Wannan nasara ta City, alama ce da ke nuna mai yiwuwa, kungiyoyin Ingila ne za su kara a wasan karshe na gasar ta UEFA.
A ranar Talata Real Madrid ta yi kunnen doki da Chelsea da ci 1-1. Madrid za ta bi Chelsea Stamford Bridge a ranar 5 ga watan Mayu.
PSG kuwa za ta yi tattaki har zuwa Etihad don sake gwada kaiminta da City a ranar 4 ga watan Mayu.
Za a buga wasan karshe a birnin Santanbul na kasar Turkiyya a ranar 29 ga watan na Mayu a filin wasa na Ataturk.