Manchester City Ta Daga Kofin Gasar Premier

Manchesyer City

A ranar Lahadi City ta doke Chelsea da ci 1-0 inda ta daga kofin duk da tun a ranar Asabar ta lashe gasar bayan da Arsenal ta sha kaye a hannun Nottingham da ci 1-0.

Manchester City ta sake lashe kofin gasar Premier a karo na uku a jere bayan da Arsenal ta sha kaye a hannun Nottingham da ci 1-0 a ranar Asabar.

City na rike da teburin gasar da maki hudu yayin da Arsenal take da wasa daya da ya rage mata.

Wannan kofi da City ta lashe shi ne na bakwai da ta samu a kakar wasanni 12.

A ranar Lahadi City ta doke Chelsea da ci 1-0 inda ta daga kofin duk da tun a ranar Asabar ta lashe gasar bayan da Arsenal ta sha kaye a hannun Nottingham da ci 1-0.