Manchester City Ke Kan Gaba

Raheem Sterling Manchester City

A cigaba da fafatawa da akeyi a bangaren tamola na kasashe daban daban a nahiyar turai, an gwabza a wasannin tsakiyar mako inda Real Betis, tayi canjaras 2-2 da Getafe.

Sai kuma ranar Asabar Valencia ta lallasa Leganes da ci 3-0, Deportivo 0-1 Atletico Madrid, Alaves, 1-0 Espanyol sai Barcelona ta doke Sevilla daci 2-1.

A ranar Lahadi kuwa. Lavente tana da 1 Girona 2, Celta Vigo 3-1 Athletic Bilbao, Villarreal 2-0, Malaga, Real Sociedad 3-1, Eibar, sai kuma Real Madrid ta samu nasara akan Las Palmas, da kwallaye 3-0.

.A saman teburin kuwa Barcelona na daya da maki 31, sai Valencia da maki 27, kungiyar Real Madrid tana mataki na uku sa maki 23.

A bangaren Firimiyan Lig na kasar Ingila kuwa a ranar Asabar an kece raini a wasanni mako na 11, Stoke city sun tashi 2-2 da Leicester city, Newcastle United 0-1 AFC Bournemouth, Swansea City 0-1 Brighton & Hove, Huddersfield Town ta doke Westbromwich kwallo 1-0. Southampton 0-1 Burnley, Westham ta sha kashi da ci 4 -1 a hannun Liverpool.

A ranar Lahadi Manchester City ta lallasa Arsenal da kwallaye 3-1, sai kuma Chelsea ta casa Manchester United, da kwallo 1-0 Tottenham da samu nasara akan Crystal palace daci 1-0 Everton ta doke Watford da ci 3-2.

Manchester City ta ke Jan ragamar teburin da maki 31, sai Manchester United take mataki na biyu da maki 23 Tottenham tana mataki na uku da maki 23.

Your browser doesn’t support HTML5

Manchester City Ke Kan Gaba - 5'45"