Tun a cikin watan Mayun bara ne dai ma'aikatan kasar suka mika wata bukatar karin albashin da ya kai na kusan Naira 56,000 ga gwamnatin da nufin rage radadin janye tallafin man fetur a kasar. Kuma an dauki lokaci ana tattaunawa a tsakanin ma'aikata da gwamnatin kafin mika wani rahoto ga gwamnatin kasar a cikin watan Afrilun da ya shude.
An sha tafka dogon turanci da muhawara a tsakanin gwamnatin da ke korafin rashin kudi da wasu jihohi da ke tafiyar hawainiya dakuma wadanda suka kasa biyan albashin ma'aikatan da ke fadi tashin tsadar rayuwa. Kuma wannan tattaunawar na zuwa ne a dai dai lokacin da tattalin arzikin tarrayar Najeriyar ke nuna alamun harbawa.
To sai dai kuma yayin da ake wannan batu manazarta na ganin akwai abun dubawa game da batun Karin albashin. Hon.Abdullahi Prembe, dan siyasa kuma masanin tattalin arziki ya ce ba karin albashi ne matsala ba, kamata yayi a dau wasu matakan kandagarki.
Shi ko Yusha'u Aliyu wani masanin, na ganin karin albashi ba shi ke kawo hauhawar farashin kayayyaki ba.
To ko ya suka ji da wannan batu? Komred Dauda Maina, shine shugaban kungiyar kwadago a jihar Adamawa, ya bayyana fatan da suke yi a yanzu.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.
Your browser doesn’t support HTML5