Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta lashe gasar Premier League na kasar Ingila bayan ta lallasa West Ham da ci 3-1 a wasan karshe na kakar bana a filin wasar Etihad na birnin Manchester.
Phil Foden, wadda ya lashe lambar yabon gwarzon dan wasar kakar bana ne ya zura kwalaye biyu a mintuna na biyu da na 18.
Sai dai jim kadan kafin ytafiya hutun rabin lokaci, Mohammed Kudus ya rama wa West Ham kwallo daya a minti na 42 da buga wasan.
Mintuna 14 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci City ta sake farkewa, wannan karon, Rodri ne ya kara zura wa City kwallo a dai dai minti na 59 da buga wasan.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin gasar da wata kungiy za ta lashe gasar so hudu a jere.
Man City ta lashe gasar a kakar 2020/2021, 2021/2022, 2022/2023 da 2023/2024, inda a kakar 2022/2023 ta lashe gasar lig lig, FA Cup da gasar zakarun turai wato Champions League.