Mallakar Katin Shaida Wajibi Ne Ga Matafiyi A Sassan Arewa Maso Gabas - Inji Soji

Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce yanzu duk wani matafiyi a jihohin Adamawa, da Borno da kuma jihar Yobe dake fama da tashin hankalin mayakan Boko Haram, dole sai ya mallaki katin shaida, wato ID Card, matakin da ta ce, ta dauka ne biyo bayan sajewa da kuma shigar da ‘yan Boko Haram ke yi cikin al'umma.

Yanzu haka ma tuni jama'a, musamman matafiya, sun fara kokawa kan abin da su ka kira tatsar da ake yi musu da sunan katin shaida.

Masu fashin baki irinsu Yakubu Uba, na ganin akwai abin dubawa game da wannan mataki da aka dauka ayanzu.

To sai dai kuma Mr. Mathew Onah, dake bin diddigin harkokin tsaro a Najeriya, ya yaba da wannan mataki da aka dauka a yanzu.

Rundunar ta sojin Najeriyan dai ta ce za ta cigaba da sa ido kan yadda jami'anta ke gudanar da ayyukansu, domin kare hakkokin fararen hula, to amma kuma ta yi gargadin da a daina bata musu suna.

Manjo Janar US Muhammad, wanda shi ne daraktan sashin hulda da fararen hula a hedikwatar tsaron kasar, ya ce, ''Bai kamata idan wasu batagari sun yi ba daidai ba, a dinga yi wa dukkannin sojojin kudin goro, hedikwatar tsaro na sa ido, domin kauce wa take hakkin fararen hula, don haka kamata yayi al’umma su bada hadin kai''.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'Aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunan Sojan Najeriya Ta Ce Dole Sai Matafiyi Ya Mallaki Katin Shaida