Ministan ma'aikatar 'yan sandan Najeriya, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya ce shugaba Muhammadu Buhari, ya yanke shawarar sake maido da ma'aikatar ne saboda bukatar da yake da ita ta ganin cewa an karfafa sha’anin tsaro.
Baya ga haka yana so a taimakawa ‘yan sanda domin su samu kayan aiki yadda za’a kara inganta sha’anin tsaro a kasar, a cewar Dingyadi.
Ya kuma kara da cewa da akwai ma’aikatar shekaru biyar da suka gabata aka rusheta kafin, amma a yanzu aka sake dawo da ita.
Kalubale Da Ke Gaba
Dingyadi ya ce irin kalubalen da yake tunanin zai fuskanta na farko bai wuce na sake gina ma’aikatar ba, na tanadar ma’aikata da wurin zama da kuma gina ma’aikatar, wanda wannan ba wani kalubale ba ne yanzu haka, domin suna nan suna yi.
Sai dai ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shi ne sha’anin tsaro, wanda Najeriya kamar sauran kasashen duniya a halin yanzu kowa na fuskantar sha’anin tsaro da ake neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mutane domin a ga an samu ci gaba da walwala mai amfani.
Ministan ya kara da cewa sun zo da wani tsari da za su taimakawa shugaban kasa na ganin cewa an samu karin zaman lafiya a kasar baki daya, kuma yana da sanin cewa ‘yan sanda suna fuskantar matsaloli da dama musamman na kayan aiki, kamar yadda shugaban kasa ya yi alkawari za’a taimaka a ga an samar.
Ya kara da cewa za a tabbatar cewa an kara jin dadinsu domin babu yadda za ka yi aiki idan ma’aikatan da kake aiki da su ba su samu walwala da jin dadin rayuwa ba.
Samar Da Kayan Aiki Ga 'Yan Sanda
Sannan ya ce za su yi kokari su ga sun tanadi kayan aiki da kuma fito da hanyoyi na zamani wanda za su sa a samu abubuwa na bayanan sirri inda za’a saka na’urar daukan hotu da dai sauransu.
A cewar ministan, zamani yana tafiya da harkokin tsaro na zamani kuma "dole ne idan za ka kyautata tsaro sai ka tabbatar da abin da suke faruwa kuma kana da kididdigarsu" sanna za ka yi maganin matsalar tsaro a kasar.
"Yanzu za ka ga yaro ya shirya yadda za’a yi garkuwa da shi domin ya samu kudi, ko kuma ka ga mutane su shirya yadda za’a yi garkuwa da su don su samu kudi ko kuma ka ga ana kai wa kauyuka wasiku domin su hada kudi ko kuma a zo a kawo musu hari."
Saurari cikakkiyar hirar da Mohammed Hafiz Baballe Ya Yi Da Ministan Yan Sanda Najeriya Muhammadu Maigari Dingyadi:
Facebook Forum