Mali Ta Kawar da Cutar Ebola

Ma'aikatan kiwon lafiya kan ebola a Mali

Ta bakin ministan kiwon lafiyar kasar Mali Ousmane Kone, kasar tayi ikirarin kawar da cutar ebola.

Kasar Mali ta ayyana cewa kasar ta rabu da cutar Ebola kwata-kwata.

Ministan kiwon lafiyan kasar Ousmane Kone wanda ya bayyana haka jiya Lahadi, yace kasar tayi kwanaki 42 babu mutum daya da aka ji ya kamu da cutar- tsawon lokaci da hukumar kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira WHO ta bayar na ayyana kasa ta rabu da annobar.

A Sabon rahoton da hukumar ta bayar tace, Mali ta dauki matakai cikin gaggawa na shawo kan cutar lokacinda aka sami rahoton mutuniya ta farko wata 'yar shekaru biyu da haifuwa wacce ta kamu da cutar da ta isar kasar daga Guinea cikin watan Oktoba.

A cikin makon jiya ma hukumar ta WHO cikin wani rahoto da ta bayar, ya nuna cewa ko a kasashen nan uku watau Guinea, da Laberiya da Saliyo, inda cutar tafi tsanani, yanzu akwai alamun ta fara lafawa.

Duk da haka hukumar tayi gargadin cewa kada a saki jiki domin cutar tana nan, kuma har tana yaduwa a wasu sassa.