Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta amshe filayen ne da gidajen mutane domin gina wata hanya da zata bi gidan kwastan har zuwa Maradi.
Za'a gina hanyar ce domin yin bikin tunawa da ranar da kasar ta samu 'yancin kai daga kasar Faransa. Daga yanzu kowace ranar 18 ga watan Disamba ranar da kasar ta samu 'yanci za'a dinga yin bikin ne a Maradi.
To saidai talakawan da aka rabasu da gonakansu, gidaje da filaye ba'a biyasu diya ba duk da cewa za'a fara aikin hanyar kwanan nan. Wata tace bata da inda zata zauna kuma bata da kudin haya. Ta kira manya suyi adalci su basu hakinsu. Su biyasu diya domin su nemi wasu filayen da zasu je su yi gini. Idan gwamnati bata shirya ta sallamesu ba sai ta dakatar da aikin har sai ta sallamesu.
Sun ji wai aiki ya kusa kawowa garesu to su suna son a biyasu sai su tashi daga gidajensu da gwamnati ta amshe.
Gwamnan jihar ya gana da talakawan wurin. Yace ba zasu yanke lokacin da za'a biya kudin ba domin kudi nada wuyar fitarwa daga gwamnati. Saidai ya umurcesu su fara kwashe kayansu daga gidajensu su nemi wuraren da zasu koma kafin a nemesu a biyasu yayin da gwamnati ta shirya. Dole su tashi domin gwamnati ta riga ta kama wuraren.
To saidai bangaren kungiyoyin fararen hula suna ganin kamata yayi gwamnati ta biya kowa hakinsa kafin su tashi.
Ga karin bayani.