Matsayar da aka cimma jama'ar kasar sun ji dadi saboda ana zaton zata kawo karshen rigingimun da kasar ta tsinci kanta a ciki musamman a arewacin kasar.
Kimanin shekaru uku ke nan ana kashe-kashen banza a arewacin kasar. Saboda haka mutane suna nuna farin cikinsu da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin kasar.
An sha kulla yarjejeniya a kasar can baya amma zaman lafiya ya zama gagarabadau saboda magabatan kasar basa cika alkawuran da suka dauka. Da ana cika alkawura can baya da zaman lafiya ya dawo kasar musamman a arewacin kasar.
A bangaren 'yan tawayen sun nemi a basu damar cin gashin kansu domin su tafiyar da harkokinsu yadda suke so a yankunansu. Sun bukaci a kara daukarsu da daraja a cikin kasar musamman hukumomin kasar domin Abzinawa ko buzaye dake arewacin kasar basu da wani tasiri. Hukumomin kasar basa daukansu tamkar wasu mutanen kwarai. Ba'a basu aiki yadda ya kamata kamar sauran mutanen kasar. Ana daukansu tamkar mutanen daji wadanda basu san komi ba.
Yarjejeniyar da aka cimma ka iya zama daratsi ga sauran kasashe dake fuskantar tawaye. Ya kamata ta nuna masu cewa kamata yayi su dinga daukan matakin rigakafi. Idan da rigakafi yakamata a dinga marawa yankunan kasashen Afirka mara domin mutane su ci gashin kansu.
Dole ne a yi rigakafi. Kada asake sai an soma tawaye da kashe-kashe ko bala'i ya taso kana a soma kokarin neman abun da ya kamata a yi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5