Kungiyar malaman makarantar reshen Makalondi ta bayyana shirin dakatar da aikin koyarwa muddin hukumomi ba su dauki matakan kare ‘yayanta ba daga abin da ta kira barazanar kisan da malaman makaranta ke fuskanta daga ‘yan bindigar jihar Tilabery.
A wasikar da ta aikewa hukumomi, kungiyar malaman makaranta ta SYNACEB ta fara ne da nuna damuwa akan halin da magoya bayanta ke ciki a karamar hukumar Makalondi da ke tazarar kilomita 100 da birnin Yamai, ta na mai cewa aikin malanta a yau a yankin da Nijer ke iyaka da Burkina wani abu ne da ke tattare da dimbin hadari.
A bayan nan ‘yan bindiga suka umurci malaman makaranta su canza aiki ko kuma su fice daga yankin kamar yadda sakataren kungiyar SYNACEB na jihar Tilabery Moussa Moumouni Mahamadou ya tabbatarwa Muryar Amurka.
Lura da irin wannan hali na zaman dar-dar din da malaman makaranta suka shiga a gundumar Makalondi, ya sa kungiyar kiran magoya bayanta su kaurace wa aiki da nufin jan hankulan hukumomi.
A sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin mahukunta da shugabanin kungiyar SYNACEB, malaman da abin ya shafa sun amince su koma kan aiki da sharadin za a ba su kariyar da ta dace.
Amma uwar kungiyar ta kasa baki daya da ke da ofishi a birnin Yamai ta gargadi hukumomi akan muhimmanci cika alkawali.
Su ma masu fafutuka a fannin ilimi irinsu Amadou Roufai Laouan Salao na kungiyar COADD, na cewa wajibi ne gwamnatin Nijar ta dauki matakai domin kawo karshen wannan matsala da ke barazana ga makomar ilimi.
Alkaluman mahukunta sun yi nuni da cewa makarantu sama da 800 ne matsalar tsaro ta yi sanadin rufe su a jihar Tilabery, lamarin da ya tilasta wa yara sama da 60,000 zaman gida kafin a watan jiya a kaddamar da wani shirin karantar da irin wadanan yara a wasu cibiyoyi na musamman.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5