Malaman Makaranta A Jihar Taraba Sun Fara Yajin Aiki

Daliban Makarantar Firamare

Hadakar kungiyar malamai ta Najeriya, NUT, ta nuna fushinta game da rashin biyan albashi na malaman makarantun firamare a jihar na tsawon watanni, lamarin da yasa malaman fusata da rufe makarantu, yanayin da yasa dalibai komawa gida.

Kungiyar malaman dai tace ba gudu ba jada baya, a wannan yajin aikin da suka fara a yau Litinin har sai an biya musu hakkokinsu.

Wannan ko ya biyo bayan rashin biyan malaman ne albashi na tsawon watanni, inda hadakar kungiyar malaman ta NUT ta rufe daukacin makarantun firamare a fadin jihar, yanayin da tilastawa dalibai komawa gida.

Haka nan kuma, kungiyar Malaman ta umarci yayanta da su zauna a gida, har illa masha Allahu, ko kuma sai yadda hali yayi.

Da yake Karin haske, game da wannan mataki da suka dauka, shugaban kungiyar malaman ta NUT a jihar Kwamred Aliyu Jauro Mafindi, ya zargi gwamnan jihar Akitet Darius Dickson Isiyaku da shakulatin bangaro game da halin da suke ciki, inda ko yace ba gudu ba ja-da- baya, wanda kuma adon haka ya shawarci iyaye das u yi hakuri game da wannan mataki da suka dauka na rufe makarantu.

To sai dai kuma,a martanin da ya maida game da wannan mataki gwamnan jihar tabakin hadiminsa ta fuskacin harkokin siyasa da cigaba, Alhaji Abubakar Bawa, gwamnan ya musanta wannan zargi inda yace za’a sasanta.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Makaranta A Jihar Taraba sun Tafi Yajin Aiki - 3'46"