A wata sanarwar da magatakardar kungiyar malaman jami’a reshen Yamai, Mohamman Kabiru Mamman, ya karanto bayan tattaunawar da ta kwashe sa’o’i da hukumomin ilimi mai zurfi, malaman jami’ar Yamai sun yanke shawarar kawo karshen yajin aikin da suka tsunduma a tsakiyar watan jiya saboda abin da suka kira yunkurin azabtar da malamin jami’a.
Malaman jami’ar dai sun daura laifi a akan shugabannin kungiyar daliban jami’ar Yamai, wadanda tuni aka kori biyar daga cikinsu daga jami’ar.
Kungiyar malaman jami’ar reshen Yamai ta bukaci magoya bayanta cewa daga yanzu su dauki dukkan matakan da suka dace domin cike gibin karatun da ya biyo bayan yajin aikin da ya shafe wata guda ana gudanarwa.
A ranar Larabar da ta gabata ne kwamitin mashawarta a jami’ar Yamai ya ba da sanarwar wasu manyan shugabannin kungiyar dalibai daga jami’ar baki daya, saboda zarginsu da yunkurin dukan wani malamin jami’a a farkon watan jiya, lokacin da ya yi kokarin ratsa wani taron ‘dalibai.
Wannan lamarin ya sa malaman jami’ar Yamai tsunduma yajin aiki na sai yadda hali ya yi.
Kungiyar dalibai dai ta kai maganar gaban shari’a, sai dai kotun ta ce daliban ba su da hurumin gurfanar da malamai a kan batun yajin aiki.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5