Malaman Jami'a Ko Su Koma Aiki Ranar Laraba Ko Su Rasa Ayyukansu

Shugaba Goodluck Jonathan ya halarci Taron Koli Na Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) a Abuja ranar 3 ga watan Satumba.

Da alama kura ta kai bango domin shugaba Jonathan ya ce ko malaman jami'a su koma bakin aikinsu nan da zuwa Laraba ko su rasa ayyukansu
Mukaddashin Ministan ilimi Mr. Wike ya ce sun sa wando kafa daya da malaman jami'a muddin basu koma bakin aikinsu ba nan da zuwa Laraba domin umurnin da Shugaba Jonathan ya bayar ke nan.

Duk da barazanar korar malaman idan basu koma bakin aikinsu ba nan da hudu ga watan nan bai hana wasu dora alhakin rikicin kan wasu wai da basu kaunar gwamnatin shugaba Jonathan ta ci nasara.

Shi kuma mai taimakawa shugaba Jonathan kan alamuran jama'a cewa ya yi tarihi ya nuna idan aka kai kowace gwamnati bango to ko tana iya daukan duk matakan da ta ga ya dace ta warware kowace takaddama. Ya ce ba laifi ba ne a kori malaman da suka yi kememe suka ki komawa aiki. Haka ma wata 'yar siyasa dake amanna da gwamnatin Jonathan, Hajiya Binta Kuraye ta ce makiyan gwamnati ne ke zuga malaman. Ta ce kila akwai wasu mugayen mutane ta bayan fagge. Suna da kudin da zasu tura 'ya'yansu zuwa karatu kasashen waje shi yasa suke zuga malaman. Ta ce kila ana bin bayan fagge ana basu wani abu domin kada a samu daidaituwa domin a lalata makarantun kamar yadda suka batasu da can. Suna yin haka ne domin a ce gwamnatin bata kwarai ba ce. Gwamnatin banza ce.

Hajiya Binta Kuraye ta ce masu yiwa gwamnati zagon kasa domin kada 'yan makaranta su koma karatu suna da yawa adanda ta kira makiyan Allah makiyan gwamnati. Ta ce sai Allah ya kamasu rana daya domin munafunci dodo ne ubangijinshi yake ci. Ta ce sai an yadda cewa ga kudin da za'a ba malamai amma wasu sai su zaga baya su zugasu jarjejeniyar da aka cimma ta wargaje. Ta ce sun dan bada lokaci kadan. Idan malaman basu koma bakin aikinsu ba za'a koresu su je su bi masu zugasu. Ta ce akwai mutane da suke da ilimi da zasu maye gurbinsu.

Masanin harkokin siyasa Buhari Bello Jega ya ce kowane sashe nada bunu a tsuliyarsa. Ya ce duk abun da ASUU ta keyi tana yi ne sabo da gyara ilimi. Ita kuma gwamnati da 'yan siyasa suna kokari ne su bata jami'o'i kamar yadda suka bata makarantun firamare da sakandare. A bangaren ASUU ya ce lallai akwai matsalolin cikin gida wanda ya kamata ta tashi ta taka rawar gani. Tana fama da cin hanci da rashawa. Akwai kuma malamai da suke lalata da 'yanmata idan ba haka ba ba zasu ci jarabawa ba.

Yanzu dai gwamnati ta umurci shugabannin jami'o'in su bude ragista domin daukan sunayen malaman da suka dawo aiki ranar Laraba. To sai dai kungiyar malaman ta ce mukaddashin ministan ilimi yana tutsi burutsu ne kawai.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Jami'a Ko Su Koma Aiki Ranar Laraba Ko Su Rasa Ayyukansu-3.16