Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Babangida Ya Nemi Gwamnati Da ASUU Su Sasanta


Janar Ibrahim Babangida mai ritaya
Janar Ibrahim Babangida mai ritaya

Tsohon shugaban kasar Najeriya ya kira gwamnati da kungiyar malaman jami'a da su yiwa Allah su sasanta rikicin dake tsakaninsu.

Janaral Ibrahim Badamasi Babangida tsohon shugaban Najeriya na soji ya yi kira ga gwamnatin kasar da kungiyar malaman jami'a ta ASUU da su kai zuciya nesa domin shawo kan tankiyar dake tsakaninsu.

Janaral Babangida ya yi furucin ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karshen mako dangane da wannan lamari. Ya ce lamarin fa ya kai intaha don haka akwai bukatar sasantawa. Ya ce ya kamata bangarorin biyu su sake rawa tun da kowanensu kasa yake yiwa aiki kuma yana son a ilimantar da yaran kasar. Wannan matsaya daya da suke da ita ya kamata ta sa su daidaita. Ya ce ba yaki ba ne. Yan makaranta sun gaji, malaman ma sun gaji kuma duk kasa ake son yiwa aiki. Don haka su zauna su warware wannan matsalar.

Dangane da zaben jihar Anambra da ya bar baya da kura Janaral Babangida cewa ya yi hukumar zaben Najeriya wato INEC a takaice, tana da jan aiki a gabanta. Idan hukumar ta san kasa take yiwa aiki kuma tana son cigaban kasar to dole ta tashi tsaye musamman da yake hukumar ta yadda an tafka kurakurai da yawa a zaben Anambra. Ya ce kamata hukumar ta koyi daratsi da abubuwan da suka faru a Anambra.

Da yake furuci game da ficewar gwamnoni biyar daga jam'iyyar PDP lamarin da ake gani babbar asara ce ga jam'iyyar sai ya ce ai hakan ya sha faruwa a lokutan baya. Ya ce shi a wurinsa ba wani abun mamaki ba ne. Duk kasar suke son su yiwa aiki kuma ba wani abu ba ne da mutum zai kasa barci a kai.

To saidai tsohon mataimakin babban sifeton 'yansanda Sanato Nuhu Aliyu cewa ya yi a wurinsu babbar asara ce kuma abu ne mai tayar da hankali matuka. Ya ce idan uwar jam'iyya bata damu ba su mabiya sun damu. Ya ce ana tafiya tare ace wasu sun balle daga tafiyar babu dadi.

Mustapha Nasiru Batsari nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG