Tun daga watan fabrairun wannan shekara daliban jami'o'in Najeriya ke zaune ba karatu saboda yajin aikin da malaman jami'o'in suka tsunduma ciki.
Daidai lokacin da iyaye, dalibai da ma wasu daga cikin malaman ke fatar ganin an kawo karshen wannan takaddama sai ga ministan kwadago na kasar Dokta Chris Ngige ya bayyana a gidan talabijin na Arise TV ranar 14 ga Yuli 2022, yana cewa malaman jami'o'in da ke koyarda kwasakwasan kiyon lafiya basu cikin yajin aiki, domin a Sokoto ma sun yaye daliban kuma shugaban jami'ar ya rubuta basu cikin yajin aiki don haka ya bayar da shawarar a soma shirin biyansu.
Kungiyar ta Malaman jami'o'in reshen jami'ar Usmanu Danfodiyo ta mayar da martani ta bakin shugaban ta Muhammad Nuradeen Almustapha inda ta ce su a matsayinsu na kungiya daya sun je sun tambata cewa, mamba su ba za su rubuta ba.
Wannan lamarin yana faruwa ne lokacin da malaman ke dakon jin ta bakin shugaban kasa, da yake kwamitin da ya baiwa mako uku ya zauna da malaman ya kammala aikinsa.
To sai dai wasu ‘yan kasa na ganin ba wannan zance ne ya dace kungiyar ta baiwa muhimmanci ba, makomar dalibai ce mafi a'ala.
Yanzu dai abin jira a gani shine martanin da gwamnati da yake kwamitin da ke sasantawa da malaman ya cimma yarjejeniya da malaman, ko dalibai zasu koma makarantu ko akasin haka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5