Malaman Jami'a Sunyi Tsokaci Kan Ranar Tunawa Da Cinikin Bayi

Ranar 23 ga watan Agusta, rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe don tunawa da cinikin bayi da haramtashi a fadin duniya. Da yake hira da Muryar Amurka yau akan muhimmancin wannan ranar, Dakta Ogbonna Onuoha na jami’ar jihar Abia dake garin Uturu, ya ce duk da cewa tun karni na 19 ne majalisar Burtaniya ta haramta cinikin bayi, har yanzu ana ci gaba da bautar da mutane a sassan duniya daban daban.

Ya ce “Ya kamata mu godewa majalisar dinkin duniya da ta mikawa duniya dokar cewa an daina cinikin bayi da bautar da mutane. Amma mun kuma lura cewa duk da haramtawar da aka yi, ana cigaba da bautarwar zamani sossai da sunar fasa-kwaurin bil’adama.

Har yanzu, ana sayan mutane don bautar dasu a wurare daban-daban, a wasuraren ma, yankasu ake yi Kuma a sayar da gabobin jikinsu a kasashen turai da kuma na nahiyar Asiya. Duniya ta san wannan na faruwa yanzu. In ba haka ba, me ke sa mutane tafiya daga kasar Libiya, daga sassan Afirka zuwa turai, zuwa da dai sauransu? Muna bukatar tambayar me yasa suke ta tururuwa zuwa kasashen ketare, kuma menene makomarsu?

Mun san ansha samun wasunsu a mace, jibge a motocin jigilar kayayyaki a kasashe daban-daban, kuma ta hakane ake rage yawan bakaken fata daga nahiyar Afirka. Ta hakane kuma ake rage wa Afirka karfi a fannonin tattalin arziki da siyasa da kuma shugabanci. Ya ce adadin ‘yan Afirka bakaken fatan da aka rasa a garin bautar dasu ya ma ninka na da.

Dakta Onuoha ya kara da cewa, ban da kebe wannan ranar don tunawa da cinikin bayi da haramtashi, ya kamata majalisar dinkin duniya ta tashi tsaye ta yaki safarar bil'adama.

Saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Jami'a Sunyi Tsokaci Kan Ranar Tunawa Da Haramta Cinikin Bayi - 3'41