ABUJA, NIGERIA - Kungiyar na cewa ba za ta sake sauraron wata tattaunawa da gwamnati ba kan yarjejeniyar inganta jami’o’i da aka cimma tun shekara ta 2012.
Shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke a zantawa da gidan talabijin na Channels ya bayyana damuwa cewa kullum bayanan gwamnati iri daya ne tun shekaru 13 da su ka wuce, sai kuma su kasa cika alkawari.
Matsayar ta ASUU na samun goyon bayan daidaikun malaman jami’ar da ke cewa gwamnati ba ta da niyyar cika alkawarin da ta dauka na biyan bukatun jami’o’in da ya sanya janye mafi tsawon yajin aikin malaman na tsawon wata tara a bariya.
Malaman na cewa ba bukatun kashin kan su ne ya sa su dagewa kan yajin aikin ba kuma da alamun gwamnati ba ta ma jin gargadin da ke haddasa rufe koyarwa a jami’o’in.
Dr. Kabiru Danladi Lawanti na jami’ar Ahmadu Bello Zaria ya tabbatar da shirin malaman na tazarce da yajin aiki matukar gwamnati ba ta biya bukatun ba.
Ministan kwadago Chris Ngige ya ce ya yi tafiya ne lokacin da kawai ya ji labari ASUU ta shiga yajin aikin na gargadi.
Ngige ya ce an dauki wasu matakan gwaji kan yanda za a biya dukkan bukatun na ASUU ga kwamitin da ya hada da hukumar sadarwar zamani NITDA.
Za a jira a ga yadda za ta kaya bayan kammalar yajin aikin gargadin na wata daya da zai kare a tsakiyar watan nan.
Saurari rahoto cikin sauti daga Saleh Shehu Ashaka:
Your browser doesn’t support HTML5