To saidai shigowar watan Ramadan na bana ya zo ne lokacin da darajar Nera ta fadi a kasuwar canji da kuma faduwar farashin gangar man fetur a kasuwar duniya da hakan ya sanya raguwar samun kudi, lamarin da ya sa har jihohi ishirin da bakwai basa iya biyan albashi.
Ganin halin da kasar ke ciki, malaman Islama sun kira al'ummar Musulmi su dage wajen yin addu'a lokacin wanna watan Ramadan don samun sauki.
Malamin Ahalu Sunna, wato IZALA, Imam Abdulahi Bala Lau, yace lokutan da suke salla su dinga addu'a Allah Ya yi jagora ga shugabannin kasar a kuma zauna lafiya a Najeriya. Ya kira 'yan kasuwa su sassauta farashinsu, kada su kula da ribar da zasu ci domin su taimakawa jama'ar Allah. Yace hatta wanda ba musulmi ba ya ga an samu sassaucin farashin kaya a wannan wata mai albarka.
Su ma dattawan arewa da suka hada da Justice Mamman Nasir na kira a yiwa kasar addu'a. Yace ba za'a yi abun kirki ba sai sun nemi zaman lafiya da yadda shugabanni zasu taimakesu. Yace su yi iyakar kokarinsu su zauna lafiya. Ya kira jama'a kada su yi fada amma su cigaba da addu'a. Ya roki Allah Ya Karawa shugabannin Najeriya basira ta yadda zasu taimaki al'ummar kasar.
Shi ma Shaikh Yakubu Musa Hassan Katsina yace a duk masallatai a dinga sanya gwamnatin Buhari cikin addu'a, musamman ma shi shugaban kasa Muhammad Buhari Allah Ya kara masa lafiya, ya bashi fasaha, ya yi mishi jagora. A yiwa shugaban kasa addu'a Allah Ya azurtashi da mashawarta na kwarai. Ya yi fatan wadanda suke yiwa gwamnatin Buhari zagwon kasa Allah Ya tona masu asiri.
Haka nan kwamishanan bincike da labaru na hukumar alhazai wanda ya ajiye aiki kwanan nan Dr.Sale Okenwa ya bayyana mahimmancin watan Ramadana ga Musulmi. Yace lokacin azumi lokaci ne da mutum ya kamata ya yi nazari akan rayuwarsa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5