Malamai sun Rike Amanar Kula da Ilmantarwa

Jami'ar Bayero Kano

Batun zargin cewa wasu Malaman manyan makarantun Najeriya, na amfani da matsayinsu wajen musgunawa dalibai, ba wani sabon abu bane, sai dai za’a iya cewa har yanzu daliban na ci gaba da fuskantar wannan matsalar a wasu makarantun kasar.

Rahotani dake fitowa daga wasu manyan makarantun kasar da suka hada da Jami’oi da Kwalejoji, na nuna cewa har yanzu ana samun abunda wasu dalibai ke kira baragurbin Malamai, wadanda keyi barazanar cutar da dalibai, idan har basu biya masu wasu bukatun su na son zuciya ba.

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa reshen Jami’ar Bayero, ta Kano, Garba Ibrahim Kunya, yace su kan ci karo da irin wannan matsalar.

Irin wannan duka da hana kuka cewar wasu ta sanya dalibai da daman a cutuwa batare da an sani ba.

Wata dalibai da ta samu kanta a irin wannan yanayi ta kuma bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa hakan na faruwa, tace “amma dana ga irin haka ya faru sai karatun ma ya fita daga kaina.”

Dr. M.D Mukhtar, wani Malami a Jami’ar Bayero, yace “mutane su kan zargi Malaman makaranta, akan tunanin suna bin wasu hanyoyi na musgunawa dalibai akan sai an samu wata dama daga wajensu sanan zasu samu jarabawan da suke nema toh, kowa nada damar ya fadi albarkacin bakinsa amma a gaskiya babu wannan abunda ake zargi akai amma da yake Najeriya, ba Jami’a daya take dashi ba, bazaka iya hana irin wannan harkar a cikin al’uma ta Jami’a ba, amma kusa kashi Tasa’in da tara cikin dari Malamai sun rike amanar da aka basu na kula da ilmantarwa.”