Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasan Video Game Na Taimaka ma Kwakwalwa Fahimta


Wasan Video Game
Wasan Video Game

A kwai tabbacin cewar, kafofin yada labarai da ma iyaye na horon yara da cewar buga wasan “video game” na haddasa dakikanci a kwakwalwar yara, kana tana daga cikin abubuwan da ke haddasa fitina a tsakanin matasa.

Duk da haka wasu bincike da aka gudanar da ke cewar, wasannin video game na tai makawa wajen haddar kwakwalwa ga yara, ba kawai wanna bama, harma da tai maka ma yara wajen lafiyar gabobi. Wasu dalilai biyar da ke nuni dacewar buga wasan video game, na tai maka wa hazakar yara.

A cewar kungiyar masana dabi’un bil’adama, ta nan kasar Amurka, buga wasan kwamfuta mai kwakwalwa, na karfafa basirar kwakwalwa da sarrafa abubuwa da kuma abubuwan da ido kan iya gani da suke kewaye da mutun.

Har ila yau tana karfafa basirar warware matsaloli, ta hanyar baiwa kwakwalwa sukunin kyautata yadda jijiyoyin aikewa da sako. Ma’ana, anan shine iya warware matsala batare da tunani mai zurfi ba a kwakwalwa, mai yin irin wanna wasan video game idan aka hada shi da wanda bai wannan wasan za'aga banban ci.

Wasan video game na tai makawa wajen samun jiki mai kamala, bisa dalilin yaro zai dinga amfani da hannu, kafafu, kai, da dai duk sauran jiki, wajen wanna wasan. Wanna wasan na kara ma yara nishani a rayuwar su a lokacin da suke wanna wasa harma zuwa bayan sun kamala wanna wasan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG