Makon Shayar Da Jarirai Da Nonon Uwa A Kano

Uwa tana shayar da jariri

An gudanar da ranar shayar da jarirai da nonon uwa na wannan shekarar a jihar kano a wani yunkuri na zaburar da iyaye muhimmancin shayar da yara da nonon uwa.
An gudanar da ranar shayar da jarirai da nonon uwa na wannan shekarar a jihar kano a wani yunkuri na zaburar da iyaye muhimmancin shayar da yara da nonon uwa.

Taken makon da aka bayar a bana shine taimakon shayar da nonon zalla kusa da iyaye wanda ke nuna muhimancin bada taimako ga iyalan masu shayarwa.

Wani rahoton da kungiyar lafiya ta fitar yace shayar da yara da nonon uwa a watanni shida na farko yana da matukar anfani ga lafiyar jarirai da samar da abinci masu gina jiki da kuma kariya daga cututuka masu illa ga kananan yara.

Wata kwararriyar likita dake aiki a asibitin kwararru na Mal Aminu Kano Dr Furdosa Aliyu El-Yakub tayi karin haske a kan batun, tace yana da muhimmanci ga jarirai da kuma mahaifiyar kanta saboda yana kare mahaifiyar a kan samun juna biyu da wuri, sannan kuma yaro zai sami lafiya sosai saboda yana kareshi daga cututuka kamar su gudawa, da kuma wadansu dabam dabam.

Dr El-Yakub ta kara da cewa, ba a so a ba jariri komi a cikin wadannan watanin shida sai nono zalla. Wadansu iyaye sun bayyana goyan baya da kiyaye wannan shawarar. Daya daga cikin matan da wakiliyar sashen Hausa Baraka Bashir tayi hira dasu tace tana shayar da jaririnta da nono zalla saboda kare shi daga kamuwa da cuttutuka.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayani A Kan shayar da jarirai da nonon uwa - 1:30