Hukumar dai ta samu tallafi daga ma’aikatar kudi ta tarayya, da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, hukumar ilimin firamare bai daya da kuma cibiyar ilimi na rundunar sojan Najeriya.
Bincike da wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya gudanar a sansanin Fofure ya gano yaran ‘yan shekara bakwai zuwa goma shabiyar na zuwa makarantun bokon ne a karon farko saboda rashin makarantu a garuruwansu na asali. Amma duk da cewar dalibai suna nuna sha’awarsu ta yin karatun Boko, matsalolin da makarantun ke fuskanta sune na iyaye da ke kin tura ‘ya’yansu makaranta, karancin kayan koyarwa da kuma rashin biyan alawus na malamai.
Sai dai duk da wadannan nasarori da hukumar ke samu a fannin ilimi, akwai wasu matsaloli da makarantun ke fuskanta. Wani malami da ya nemi muryar Amurka ta sakaya sunansa ya ce rabonsa da a biya shi kudin alawus watanni bakwai da suka gabata, a bangaren iyaye da daliba kuma inji shi suna anfani da dabaru na laluma waje jan hankalin yara zuwa karatu a makarantar.
Malam Sa’ad Bello shugaban hukumar kai dokin gaggawa ta kasa na jihar Adamawa ya shaidawa wakilinmu cewa baya ga ciyarwa hukumar tare da tallafin ma’aikatar kudi ta tarayya tana daukar dawainiyar kudin makaranta, sufiri, kudin guziri da baiwa iyaye damar ziyartar ‘ya’yansu a makarantun da suke karatu.
Wata daliba mai suna Hauwa Yusuf ta kwatantawa Sunusi Adamu irin darusan da ake koya masu sai dai fargabar da ake da ita ce ta makomar karatun bokon wadannan yaran, idan suka koma garuruwansu na asali inda babu makarantun boko.
Saurari cikakken rahotan Sunusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5