Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Hukumar SSS Nada Ikon Rufe Ofishin Kasafin Kudin Majalisar Wakilai


Dogara Yakubu, kakakin majalisar wakilan Najeriya
Dogara Yakubu, kakakin majalisar wakilan Najeriya

Batun aringizon da ake zargin an yi a majalisar wakilan Najeriya sai dada rincabewa ya keyi duk da cewa 'yan majalisar na hutu.

Abun da ya fi daukan hankalin jama'a yanzu a Najeriya shi ne damar da hukumar tsaro ta SSS ta samu har ta shiga harabar majalisar wakilai ta rufe ofishin kasafin kudi.

Jama'a na tunanen cewa kundun tsarin mulkin Najeriya ya rabawa kowa abun da zai yi.

Barrister Mai Nasara Umar kwararre akan harkar shari'a musamman kundun tsarin mulki ya yi bayani. Yace akan zarge-zargen da aka yi hukumomin tsaro nada 'yancin da zasu shiga harabar majalisar, shiga kowane ofis su yi bincike akan korafin dake gabansu.

Suna kuma iya shiga domin su kare wasu takardu ko naurorin bayanai tunda wadanda suke ofishin suna cikin mutanen da ake zargi. Idan basu kare wasu takardu ko naurori ba wasu na iya daukesu ko su share wasu bayanai cikin naura. Idan ko sun dauke wasu takardu ana iya samun rauni idan batun ya kai gaban kotu.

Onarebul Magaji Da'u Aliyu yace daya daga cikin babban aiki shi ne a zauna lafiya. Idan su SSS sun shiga su kare wurin ne sun kyauta. Idan sun yi ne su kare mutuncin majalisa yace yana goyon bayan abun da suka yi.

Yanzu dai hukumar SSS ta rufe ofishin kasafin kudin majalisar da na shi Abdulmummuni Jibrin.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG