Majalisun Najeriya Nada Hurumin Kara ko Rage Kasafin Kudi-Ndime

Sanata Ali Ndime, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa

Bayan kokarin da shugabannin majalisa ke yi na wanke kansu daga zargin yiwa kasafin kudin bana coge, ana cigaba da samun masu mara baya kan lalle a gudanar da binciken lamarin da suke ganin a matsayin mummunar dabi'a ta almundahana tun shekara ta 2003

Gajiya da zargin tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai ya sa shugaban mara sa rinjaye Ogoh yayi barazanar gufanar da shi Jibril Abdulmummuni gaban kuliya.

Ogoh yace Jibril Abdulmummuni ya yi masa sharri domin ya yi zargin wai shi Ogoh ya yi aringizo akan kasafin kudin ma'aikatar Niger Delta na wasu biliyoyin nera.

Ogoh yace dabi'ar birkita kasafin kudi ya sa Jbril Abdulmummuni rasa kujerarsa wanda kuma shi a matsayin maida martani ya juya ya kirkiro bayanan bogi da zummar bata suna.

Amma shi shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Muhammad Ali Ndime cewa yin kari ko rage kasafin kudi ba laifi ba ne kuma ba abu ba ne da 'yan majalisa zasu shiga kasuwa suna cerere akai ba.

Shi kuwa dan majalisa a inuwar PDP Ismaila Muazu Hassan kare kakain majalisar wakilan ya yi tare da cewa duk wani matakin da majalisar ta dauka na kan doka. Kundun tsarin mulki ya ba majalisun damar su duba ,su gyara, su kara ko su rage. Yace idan an kara ko an rage ya zama "padding" a wurin wadanda basu san lamarin ba gaba daya.

To saidai matasan APC sun ce 'yan majalisa sun saba bin bahaguwar hanya. Saboda haka shi Jibril ya ga gara ya fasa kwai domin ya nemi hanyar fita domin al'ummar kasa su goyi bayanshi.

Hukumar EFCC ta fara binciken lamarin amma a majalisar wakilai.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisun Najeriya Nada Hurumin Kara ko Rage Kasafin Kudi-Ndime - 2' 38"