Majalisun Kasashen Afirka Ta Yamma dake Anfani da Kudin Sefa Sun Yi Taro A Nijar

Kwamitin kasashen yankin Afirka ta Yamma renon Faransa

Abubuwa ukku ne masu mahimmanci suke kan gaba a wannan taron na majalisun kasashen yammacin Afirka masu anfani da sefa da kuma harshen faransanci.

Wannan kasashen dake anfani da sefa yau al'ummominsu na dandana kudarsu sakamakon rigingimun da suka addabi kasashen nasu.

'Yan ta'ada na cigaba da kai hare khare cikin kasashensu. Kasashe irinsu Mali, Nijar,Ivory Coast, da Burkina Faso sanadiyar rikicin Boko Haram a Najeriya da wasu a cikin wasu kasashen.

Haka ma a wasu kasashen ana fama da rikicin cikin gida saboda kwamitin ke shirin daukan wasu matakan shawo kan lamarin. A cewar Fatima Dubu Dogo mataimakiyar shugaban kwamitin din majalisun tace suna fadakar da kansu ne akan yadda ake shirya kabilun dake fada tsakaninsu. Akwai bukatar a san yadda ake shawo kan 'yan ta'ada.

Ga rahoton Sule Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisun Kasashen Afirka Ta Yamma dake Anfani da Kudin Sefa Sun Yi Taro A Nijar - 2' 45"