Majalisun Dokokin Amurka Sun Dauki Matakin Kaucewa Rufe Gwamnati

Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Majalisun dokokin Amurka na gab da yarda da tsarin wucin gadi na kashe kudaden gwamnati don gujewa dakatar da harkokin gwamnatin kasar.

Gaba dayan majalisun na dattawa da wakilai suna shirin sa hannun ne ga kasafin kudin da zai dau nauyin ma’aikatun gwamnatin tarayya har zuwa ranar 11 ga Disamba.

Wannan kada kuri’ar akan kudurin na wucin gadi da ‘yan majalisar za su yi, shine zai bada damar ci gaba da kashe kudi kasancewar watanni 12 na kasafin shekara da ya zo karshe.

Shugaba Obama dai da ‘yan jam’iyyarsa da ke Majalisun, sun sha karawa da ‘yan jam’iyyar adawa ta Republican game da ayyukan gwamnati.

Su ‘yan Republican sun fi damuwa da ganin an kashewa harkokin soji da kuma shirye-shiryen da suka shafi na tsaron cikin gida.

Su kuma ‘yan Democrat sun fi son ganin an kashe kudade akan manyan kwangiloli da kuma ayyukan inganta jin dadi da rayuwar al’ummar kasar.