Majalisun Amurka Sun Dau Matakin Kaucewa Sake Rufe Gwamnati

President Donald Trump

Masu tattauanawa majalisun dokokin Amurka sun cimma babbar yarjejeniya a kan bada kudaden gudanar da ma’akatun gwamnati tarayya domin hana sake rufe su a karshen wannan mako.

‘Yan kwamitin majalisa a kan lamarin sun bayyanar da yarjejeniyar ga jama’a, amma kuma wasu hadiman majalisun tarayyar sun ce yarjejeniyar ta hada da dala biliyan 1 da miliyan dari hudu na gina sabuwar kantanga mai tsawon kilomita 88 a kan iyakar Amurka da Mexico. Akwai kuma batun inganta fasahar tantance masu shigowa kasar a kan iyakar da kuma kara yawan ma’aikatan kostom da kayan taimako.

Watanni da dama shugaban Donald Trump yake bukatar dala biliyan biyar da miliyan dari bakwai ya gina Katanga, yayin da ‘yan Democrats suka kira bukatarsa da barna, mara amfani kuma suka ce zasu amince da kudaden tsaron iyaka amma ban da gina Katanga.

Wannan yarjejeniya da aka cimma cikin gaggawa na nuna kowa ya sassauto a kan matsayinsa.