ZABEN2015: Majalisar Kasa Ba Zata Yiwa INEC Katsalandan Ba - inji IBB

Tsohon shugaban Najeriya Janaral Ibrahim Badamasi Babangida

A cikin firar da yayi da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Alfa Ahmed, Janaral Babangida yace majalisar kasa ba zata yiwa hukumar zabe katsalandan ba.

Janaral Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya yace lokacin da suk yi taron kasa hukumar zabe ko INEC a takaice tana zaman kanta sabili da haka ba zasu iya gaya mata abun da zata yi ba sai dai su bada shawara bisa ga yadda doka ta tanada.

Tsarin mulkin kasa ya ba hukmar ikon ta shirya yadda zata yi zabe sabili da haka ba daidai ba ne su gaya mata abun da zata yi.

Shugaban hukumar zabe ya fadawa majalisar kasa duk abubuwan da suka yi kuma inji Janaral Babangida sun yi kokari. Amma akan matsalolin da suka taso sun umurci shugaban hukumar ya koma yayi magana akai. Daga baya ya koma taron ya bayyana masu. Janaral Babangida yace duk abun da ya fada masu basu da dama su ce masa a'a.

Dangane da barazanar da wasu magoya bayan 'yan takaran APC da PDP keyi cewa idan dan takararsu bai ci zabe ba zasu tada rigima, sai tsohon shugaban yace dama irin wadannan maganganun na tasowa. Dalili ke nan da aka yi taron 'yan takaran inda Janaral Buhari daga APC da shugaba Jonathan daga PDP suka sa hannu a yarjejeniya suna neman a yi zaben lafiya. Yin hakan ya nunawa magoya bayansu cewa basa son rikici.

Janaral Babangida yace duk kasar da ake siyasa akwai maganganun tashin hankali na faruwa kuma babu wanda zai ce yaki yana da anfani. Ahalin yanzu, inji Janaral Babangida yana ganin kowa ya san anfanin zaman lafiya kuma babu yadda kasa zata ciga ba tare da zaman lafiya ba.

Duk wanda yayi imani cewa 'yan Najeriya basu da wata kasa da ta fita to ashe kuwa ba za'a yi abun da zai kawo wargajewarta ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Kasa Ba Zata Yiwa INEC Katsalandan Ba- inj Janaral Babangida - 4' 43"