'Yan majalisar dai sun ce sun dauki wannan matakin ne domin kare muhalli daga gurbacewa wanda kasashen duniaya da dama ke kokarin yi, duba da illar dake tattare da leda a koramai da tafkuna da kuma karkashin kasa.
Dokar dai na cewa duk wanda aka samu ya karya ta, ba shakka za’a yanke masa hukuncin daurin shekaru uku, ko ya biya tarar rabin miliyan na naira, ko kuma duka.
Wani mai amfani da ledar a Najeriya, yace ya goyi bayan matakin domin su ma zasu sami sauki wajen hada hadar kasuwanci. Shi kuwa wani mai kanfanin leda mai suna Ibrahim Mai Leda, cewa yayi wannan mataki bai dace ba, ina laifi a ce duk wanda ke son sayen leda a kara masa kudi mai makon kyauta da yanzu ake bayar wa. ya kuma ce tabbas za’a fuskanci matsalar rashin aikin yi daga kanfanonin leda.
Shi kuwa a bangaren sa Malam Muhammed Sani, wani Malamin kimiyayya,
cewa yayi matakin zai taimaka wajen rage ledar da ke cika magudanan
ruwa tare da gurbata muhalli. A cewar sa leda kan dauki shekaru kafin ta narke a kasa, abinda ke haifar da gurbacewar kasa da kuma yanayi.
Yanzu dai abin jira a gani dai shine ko dokar za ta yi tasiri a
Najeriya idan aka amince da ita bisa la’akari da kaka-gidan da leda tayi a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton wakilin Murya Amurka Babangida Jibril.
Your browser doesn’t support HTML5