Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya bayyana wa taron manema labarai na mussaman cewa, sanin halin da jama'a ke ciki ya sa dole su dauki matakan gaggawa na magance yunwa da hauhawan farashin kayayyaki da suke kara sa kunci a rayuwar jama'a.
Ko da yake bai fadi takamaman lokacin da za a fara shimfida tabarmar saukin ba, Tajudeen ya ce za a dauki matgaki nan ba da dadewa ba, domin bukatar yin haka ta taso.
Kakakin Majalisar Wakilan ya jaddada cewa, Majalisa za ta cigaba da daukar matakai kan batutuwan da suka jibanci yalwar abinci da kuma sha'anin tsaro yadda manoma za su iya komawa harkar noma kamar yadda aka saba.
Tajudeen ya ce lokaci yayi da Majalisar za ta fara hukunta manyan jamia'n tsaron da suka kasa iya rike amana ta kasa
Bisa ga cewarsa, Majalisar na sane da kalubalen tattalin arziki da 'yan kasa ke fama da shi, kuma tuni su ka fara daukar matakai a wannan fanin inda ya ce sun himmatu wajen shawo kan koma bayan tattalin da mayar da kasar kan turbar cigaba mai dorewa. Tajudeen ya ce batun karancin abinci da ake fama da shi yana zuciyar sa domin samar da abinci shi ne abu mai muhimmanci ganin cewa rashin abinci yana da alaka da harkar tsaro.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a fito da hatsi iri daban daban har ton dubu 42,000 na masara, gero da sauran kayan masarufi a cikin tsare tsare don magance tashin farashin kayan abinci a kasar.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5