Majalisar Wakilan Najeriya Na Binciken Abin Da Ya Faru a Afirka ta Kudu

Majalisar wakilian najeriya

A Najeriya Mahukunta na ci gaba da kokarin gano musababin kisan gilla da aka yi wa yan Najeriya fiye da 80 a Johanesbourg ta Kasar Afrika ta Kudu.

Jagoran tawagar kuma shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na Majalisar Wakilai Onorabil Yusuf Buba Yakubu, ya ce Majalisa ta kyamaci wannan mummunan al'amari da ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya da ke kasar Afirka ta Kudu.

Shugaban yace Majalisar ta yi Allah wadai da wannan ta'asa da aka yi duk da cewa Najeriya ita ce kasa da ke kan gaba wajen taimakawa Afirka ta Kudu, a cikin Kasashen da ke Nahiyar a lokacin da take bukatar taimako.

Hakazalika shugaban hukumar sa ido a akan 'yan Najeriya da ke kasashen ketare Abike Dabiri Erewa, ta ce bata ga dalilin da zai sa jami'an tsaron Afirka ta Kudu su kasa fitar da kwakkwaran rahoto akan aukuwar irin wannan barazana ba, har ma da wanda suka faru a baya da ke bukatar wani bayani da zai bada alkiblar daukan matakan da suka dace.

Shima mai nazari akan harkokin dangantakar kasashe Ahmed Mohammed Alkali na da ra'ayin ganin kasashen biyu sun yi sulhu ba tare da bata lokaci ba.

Wannan barna dai da aka yi wa 'yan Najeriya ba shi ba ne karo na farko ba, kuma ya sa wasu 'yan Najeriya a nan gida sun dauki fansa akan harkokin kasuwanci da ke da alaka da Afirka ta Kudu.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Wakilan Najeriya Za Tayi Tattaki Zuwa Afirka ta Kudu