ACCRA, GHANA - Idan fadar majalisar muddin gwamnati bata saka kimanin sidi miliyan sittin da bakwai na Ghana a asusun tallafawa daliban ba, daliban baza su samu abinci ba.
Hakan kuwa zai sanya rashin neman ilimi a kasar cikin yanayin koma baya ijnji wasu masu sharhi kan lamura ta kamar Mallam Bashir Abdul Hamid malami a kolejin Atebobo College of education.
A hirar shi da Muryar Amurka, mai magana da yawun kungiyar hadin guiwan dalibai masu karbar horsawa a kolejojin fadin kasar Usman Salisu Bamba ya bayyana cewa, tuni wasu dalibai a makarantu suka fara kokawa kan jinkirin samar masu da alawus-alawus, abinda suka ce ya gurgunta tattalin arzikinsu.
Sai dai ministan ilimi a kasar Dr. Yaw Adutwum ya gana da manema labaru ajiya inda ya ce biyo bayan kokawan majalisar shugabannin kolejojin, gwamnati ta fara biyan wadannan kudade.
Majalisar na dogara bisa tallafin da gwamnati ke samar wa daliban da suke samun horaswa a kolejin malamai ne, gurin ciyar da su, don haka rashin tallafin ka iya janyo matsala.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam Kumasi Ghana:
Your browser doesn’t support HTML5