A wani zama na takaitacen lokaci da 'yan majalisar suka yi a garin Lafiya sun baiwa alkalin alkalan jihar mako guda kan ya nada kwamitin da zai gudanar da bincike akan zarge-zarge goma sha shida da suke yiwa gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Muhammed Baba Ibaku yayi karin haske akan zaman nasu. Yace su 'yan majalisa ashirin da masu yaki da cin hanci da rashawa hudu ko EFCC suka zauna a majalisar. Sun ba alkalin alkalan jihar umarni ya nada kwamiti mai mutane bakwai da zasu duba zargin da suke yiwa gwamnan kamar yadda doka ta tanada.
Doka ta ba alkalin alkalan mako daya ya kafa kwamitin. Bayan ya nada, kwamitin nada wata uku ya kammala aikinsa. Amma suna iya su gama aikinsu cikin sati daya ko kwana uku.
Yayin da 'yan majalisar ke cikin majalisar wasu matasan APC sun tafi harabar majalisar. Alhaji Abdulkarim Allah Nanan Keana shugaban matasan APC yace da safe suka samu labarin cewa 'yan majalisa suna zaman tsige gwamnan jihar sai suka yi dafifi zuwa majalisar. Amma da yansanda suka gansu sai suka soma harbi na kan maiuwa da wabi. Matasa biyu sun samu rauni.
To amma kakakin 'yansandan jihar ASP Ismaila Umar Kwa yace babu wata matsala da aka samu a harabar majalisar.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5