Majalisar Dokokin Ukraine Ta Soke Zamanta Kan Barazanar Harin Rasha

Majalisar Dokokin Ukraine

Kyiv ta rufe Majalisar Dokokinta tsawon yini guda a yau Juma’a, saboda yiyuwar kai harin makami mai linzami bayan gargadin da Shugaba Vladimir Putin ya aikewa kasashen yammacin duniya ta hanyar harba sabon makami mai linzami mai cin matsakaicin zango daka iya goya nukiliya a kan Ukraine

Mamayar watanni 33 da Moscow ke yi a Ukraine ta sake zafafa a makon da muke ciki sakamakon kaddamar da makami mai linzami mai cin matsakaicin zango daka iya goya nukiliya da Rasha ta yi a karon farko kan birnin Dnipro a jiya Alhamis.

A yau Juma’a, fadar Kremlin ta bayyana cewar Amurka ta fahimci sakon dake cikin kakkausan jawabin da Putin ya gabatar, wanda a cikinsa ya yi barazanar kai hari kan kasashen yamma tare da jaddada cewa a shirye yake ya tunkari kowane irin yanayi.

Putin ya kara da cewar moscow nada damar kai hari kan kasashen da suka sahalewa kyiv kai hari cikin rasha da makamansu, bayan da amurka da burtaniya suka baiwa kyiv iznin yin hakan.

Rundunar tsaro ta NATO da jami’an Ukraine za su gana a Talata mai zuwa a birnin Brussels domin tattaunawa a kan kazantar rikicin, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiya suka shaidawa kamfanin dillancin labaran afp.

A birnin Kyiv, wanda ya sama fuskantar hare-hare daga jirage marasa matuka da makamai masu linzamin Rasha, majalisa ta soke zaman da ta saba gudanarwa a kowace juma’a domin mika tambayoyi ga gwamnati a kan fargabar kawo hari.